Wata mata da take zuwa gidan yari cikin sirri take shayar da mahaifinta ruwan nononta domin kada yunwa ta kashe shi.
Koda yake nasan mutane da yawa abubuwa zasu zo cikin zuciyarsu daga zarar sunga wannan photon na yadda wata mata ke shayar da ruwan mamanta ga wani tsoho mai tarin shekaru, wasu ma za suce kamar wani salo ne na iskanci.
To saidai wannan photon da kuma labarin bashi da wata alaka da iskanci ko kadan.
To saidai duk lokacinda mutum ya saurari wannan labarin watakila zayyi kuka ne da idanunsa harma hawaye masu yawa su fita daga cikin idanunsu.
Wasu kuma koda basu yi kuka ba za suji tausayin abin.
Labari ne daya faru a gaske na wata mace da tayi ta shayar da mahaifinta ruwan nononta lokacin da aka kulle shi a gidan yari domin ta kare shi daga hukuncin da aka yanke masa na kisa ta hanyar yi masa horo da yunwa harya mutu bisa satar bread da ya aikata, abin ya faru ne tun a karni na goma sha bakwai a birnin rum.
Laifin aikata satar bread yasa aka yanke masa hukunci mai tsauri na horo da yunwa harya mutu a gidan kurkuku.
Mutumin mai suna cimon shine aka kama da aikata wannan laifin kuma shi aka yankewa wannan hukuncin.
Yar gidan wannan mutumin mai suna pero tayi iya bakin kokarin ta ganin masu kula da gidan yarin sun amince akan ta kaiwa mahaifinta ziyara daga karshe suka amince da sharadin zata shiga amma ba tare da taje da komai na daga dangin abinci ko abin sha ba.
Take ta amince da batun domin ita dai tafi so ne kawai taga mahaifinta sannan taga halin da yake.
Bayan ta shiga ne ta iske shi cikin wani yanayi na galabaita wanda zai iya mutuwa kowanne lokaci saboda yunwa take ta kama kansa ta fara shayar dashi.
Domin ganin mahaifinta ya rayu haka taci gaba da zuwa gidan yarin tana shayar da mahaifin nata nono a haka har aka dauki lokaci mai tsawo ba tare da ya mutu ba.
Abin ya bewa mutanen dake kula da gidan yarin mamaki ganin har yanzu bai mutu ba.
Dan haka suka kulla wata dabara suke buya idan har pero zata shiga gurin mahaifinta da haka har suka kamata akan cewa ita ce ke shayar dashi.
Daga karshe dai saboda tausayi yasa aka saki wannan tsohon.
Comments
Post a Comment