Abubuwan birgewa game da kasar Nigeria.
Akwai abubuwa na birgewa masu tarin yawa wanda kasar Nijeriya take dasu wanda kusan ba kowacce kasa bace take da irin wadannan abubuwan ba a nahiyar Africa dama sauran kasashen duniya baki daya.
Nigeria kasa ce da take da manyan abubuwa na gani na fada, wannan yasa a Africa take zuwa ta farko a wasu abubuwa idan har za'a kwatanta ta da sauran kasashen.
Yau cikin shirin namu muna tafe ne da jerin abubuwa kala kala wanda kasar Nijeriya take dasu na birgewa.
✓ Yawan jama'a:- Ko kunsan kasar Nijeriya tana ta daya daga cikin kasashe mafiya jama'a a kaf Africa? Wannan ma wani abin birgewa ne domin kasar tayiwa sauran kasashen fintinkau ta bangaren mutane.
✓ Yaruka masu yawa:- kasar Nijeriya tanada yare da yan kasar suke amfani dashi yakai dari biyar, wannan shine ya bada tabbacin tanada kabilu masu yawa wanda da wuya a samu kasar da ta kaita ko kuma ta fita a yawan kabilu.
✓ Masu arziki da tarin dukiya:- Akwai mutane masu matukar arziki a kasar wanda kusan babu kasar da ta tara masu arziki kamar Nigeria a yanzu domin mutum na farko da yafi kowa arziki a Africa dan kasar ne wato Aliko dangote.
✓ Wayewa:- Kusan da wuya cikin kasashen Africa a samu kasashe goma ko biyar da yan kasar suka fi yan Nijeriya wayewa domin duk wani guri a duniya da wuya kaga ba'a damawa da dan Nigeria a ciki.
✓ Malaman addini:- Idan batun tarin malamai ake to Nigeria tana sahun farko a duniya baki daya bama Africa ba, domin akwai malaman addini masu yawa a kasar.
✓ Kasuwanci:- Kusan Nigeria ce cibiyar kasuwanci a Africa duk da akwai kasashen da suma ba a barsu a baya ba amma dai Nigeria tanada hanyoyin kasuwanci masu yawa domin tana fitar da albarkatun kasa zuwa kasashen ketare.
✓ Jami'an tsaro:- Kusan Nigeria tanada jami'an tsaro na bangarori da dama wanda kusan kaf Africa babu kamarta.
✓ Masu amfani da wayar hannu:- An fibayyana kasar Nijeriya a matsayin kasar da mutanen cikinta masu yawa ne ke amfani m da wayar hannu wannan yasa aka samu matasa masu dinbin yawa suke ci kuma su sha ta bangaren yin kasuwanci da wayoyin hannunsu.
√ Kyawawan mata: Nigeria na daya daga cikin kasashe da suka tara mata masu kyau fasali da diri sannan da tsafta, duk da a Africa akwai kasashen da suka fita mata masu kyau amma dai idan za'a lissafa kasashe masu mata masu kyau to akwai Nigeria.
Wannan sune kadan daga cikin abubuwan birgewa a kasar Nijeriya dan haka ku bayyana mana sauran ta akwatin comments dinku.
Comments
Post a Comment