Istimna'i zinar hannu da matsalolin da take haifarwa jiki
Yanzu mun shiga wani zamani mai wuya wanda abubuwa suke ta yawan faruwa tsakanin matasa maza da mata, wanda bashi da kyau sosai
Wanda zaka samu mutane da dama kan biyawa junansu bukata ta hanyar amfani da hannunsu ko wani abu daban dan gudun kar suje su aikata Zina to wannan shine ake kira istimna'i..
Wanda yin hakan ba karamar illa bane ga lafiyar mutum sannan a addini ma bai halatta ba kamar yadda malamai da yawa sukai bayani
Wasu daga cikin illolin da aikata zinar hannu ke haifarwa
1.Saurin inzali.(Premature ejaculation)
2.Rashin karfin zakari.(soft and weak erection)
3.Digowar maniyi a yayin fitsari ko bayan gari(semen leakage)
4.Low libido (karamcin sha'awa)
5.Tsananin kasala (fatique)
6.Saurin manta abu ko riqe karatu (forgetfulness and lack of confidence)
7.Saurin kwanciyar zakari (short term erection)nan take zakari da ya tashi baya jimawa sai ya sake kwantawa.
8.Bayan gari mai tauri (constipation)
9.Kamkamcewar gaba (smallness of penis) kaikace na karamin yaro ne.
10.Rashin ruwan maniyi masu kauri (thin semen fluid)
Matakin da zaku bi idan kuna aikata zinar hannu
Mataki na farko anan shi ne ka canza tsarin rayuwarka gabaki daya waton life style.
Ka nisanci duk wani abu da zai sa kayin istimna'i.
Magangannun batsane kalle kallen hotunan fitsara da dai makamantansu.
Ka rinqa cin abinci mai gina jiki (balancediet) . A hakika abinci na daya daga cikin manya manyan abubuwa masu taka rawa ta musamman dan samarda jini da maniyi ga jikin dan adam.
Dan haka a rinka cin abinci mai daukeda sinadirran dake da alfano ga jiki,kama daga sinadiran dake inganta lafiyar koda,zuciya da qwaqwalwa gami da na lafiyar mazakutar namiji(reproductive system)
Abinci da dama da muke ci muna cine kawai dan maganin yunwa amma a hakikanin gaskiya ba wata martaba yake yiwa jiki ba,baya daukeda nutritional values din da jiki ke bukata.Sai kaga anci abinci amma ana ta faman zuwa toilet saboda baya da wani amfani ga jiki.
Bawai sai abinci mai tsada keda vitamins ba,da dama muna ganin kamar sai mai hali ke iya cin abinci mai sinadiran dake gina jiki; wannan ba haka bane.Misali ga su zogale wallahi ba karamin taimakawa jiki ta ke yi ba.
Ga su ganyen alaiyafu da wake a rinka dafawa ana ci.
Ga kwai wanda aka dafa duka guda daya zuwa biyu ya wadatar ba abinci bane da za a zauna ayiwa cin tuwo abinda ake bukata kawai a rinqa ci akai akai amma bada yawa ba,dan shi abinci nau'in protein baya bukatar aci sa da yawa yana iya haifarda gudawa ko lalacewar ciki.
Kamar dangin kwai(eggs) Nama,madara, kifi (fish),beans(wake).
Sannan ka dinga shan diyan itatuwa fiye da abincin da kake ci :
Saboda jikinka ya rasa wasu muhimman sinadirai wadanda suna nan a cikin maniyin da kake ta zubarwa akai akai,wanda diyan itatuwan kawai zasu taimaka maka ka samu damar dawowa da wadannan sinadiran da ka rasa.
Haka kuma cutukka da dama da basa jin magani ana warkardasu ta yawan shan diyan itatuwa a hakika akoi fa'ida sosai ga haka
KAMARSU
lemu,cashew,abarba,kankana,karas,kwakwa da kuma shan ruwanta,ayaba, inabi,tuffa,da dai sauransu.
Harwa yau za a iya amfani dasu coconot oil
,cheese,peppers,zinc
,strawberries,flax seeds,kidney beans,da kuma avocadoes.
ABINDA ZAKA NEMA
ka nemi wadannan magungunnan da ake kira da natural medicines wadanda basu da wani lahani a jiki dukansu daga tsirran itatuwa ake yinsu.
Pine pollen and maca root powder.
Tribulus trestiries.
Libido booster
Horny goat weed.
L-Arginine.
Zaka iya amfani da biyu ko uku a lokaci guda amma kada ka nemi wadanda ba su ba.ka tabbatar sune ka siya dan idan baka san products din ba to za a iya baka wadanda ba su ba wanda wani lahanine daban kuma ba zasu amfaneka ba.
Mataki na karshe sai a rinka motsa jiki sannan ana samun bacci.
Comments
Post a Comment