Kasashe biyar da suka fi Samar da mai a Africa
Barka da zuwa wannan gidan, gidan da yake kawo bayanai akan wasu abubuwa da suka faru ko suke faruwa a Nahiyar Africa dama Duniya baki daya.
Yau cikin shirin namu zamu kawo muku jerin wasu kasashe ne guda biyar da aka bayyana sunfi kowacce kasar Samar da mai a Nahiyar Africa dan haka ga jerin su nan.
Nigeria :- Kasar Nigeria kusan ita ce kasa ta farko a Nahiyar Africa wajen samar da Mai, kamar yadda aka ce tana samar da wajen ganga mai yawan gaske a rana daya, wannan yasa ta zamto kasar da ta rike tuta a matsayin ta farko
Algeria:- Kasar Algeria ita ce ta biyu kamar yadda bincike ya nuna a samar da mai sannan ita ce babba inka dauke kasar Nigeria domin tana samar da ganga masu yawa a rana.
Libya :- Kasar Libya ta rike tutar mataki na uku a jerin kasashen Africa da suke samar da Mai domin ance kasashe biyu ne kawai a gabanta a kaf Nahiyar Africa wato Nigeria da kuma Algeria
Angola:- Wannan kasar ta zamto kasa ta hudu a cikin Africa wajen samar da mai domin ance tana samar da ganga masu yawa a kowacce rana.
Egypt:- Kasar masar ko kuma muce kasar Egypt ta zamto kasa ta biyar wajen samar da mai a Nahiyar Africa
Comments
Post a Comment