Matar da aka tilasta saita saka takunkumin karfe (facemask) tsawon shekaru 80 saboda kyawunta
Ko kunsan akwai matar da aka tilastawa sanya takunkumi a fuskarta har tsawon shekaru tamanin saboda kyawun da take dashi?
A zamanin baya bayi basu da wata dama a gurin Ubangidansu dole duk wani umarni daya basu dole su bi ko da basa so haka zasu yi.
A irin wannan karnin ne akai wata budurwa wacce ta kasance mai tsananin kyau na ban mamaki wanda takai ta dare kowa a fadin gurin da take saidai kuma kash baiwa ce da take gurin wani.
Kamar yadda kuke gani a photon, wata mata ce sanye takunkumi a fuskarta..
Ita dai wannan matar sunanta Escrava Anasticia, wanda aka mayar ta baiwa, wanda a farko bata kasance baiwa bace, ta rayu ne a kasar Brazil a ƙarni na goma sha tara(19th century.
Anasticia wanda ta sharara wajen kyawu, da kuma kyawawan idanu masu launin shuɗi jajirtaciyace gata kuma da tsananin so da kuma kaunar addini kamar yadda wasu mutanen suke fada wadda ta kasanc ƴar ƙabilar "Rio da Janeiro" ce.
Mahaifiyarta Mai suna Delminda ƴar Nahiyar africa ce kuma baiwa da aka kama, aka mata ƙarfa-ƙarfa kana aka sayar da ita ga wani dillalin bayi a waccan lokacin domin boye rashin adalcin da aka mata a tsawon lokacin rayuwarta.
Escrava kuwa ba daɗe da sayar da mahaifiyarta ba aka haife ta. Ta kasance abar kwatantace ga kaf fursunonin da suke tare a wannan lokaci domin tsananin kyanta, da kyawun shuɗayen idanunta, da kuma ɗaukar hankalin kowa da take idan sun ganta.
Wannan yasa aka sanya mata takunkumin daya rufe fuskarta domin a batar da kyawunta wanda yake birge mutane.
Sannan aka fara gana mata azaba iri iri bayan tsananin wahala, da azabtarwa da ta sha wajen abokan zaman ta tunda ta kasance mai kyawun daya dara nasu sai kuma Karin azabtarwar da take sha a wajen Ubangidanta Jaoqyin Antonio.
Domin wani ƙaton sasari(iron collar) aka sanya mata a wuya, hakan ya yi sanadiyyar shaƙe wuyanta magana bata iya yi sai dakyar. Batun abinci kuwa sau ɗaya ne ake bata dama ta ci a rana ta fuskanci tsananin takura da musguwana wadda har ta gwammace barin duniya.
Kullum canza nau'in azaba ake mata, ga wata makekiyar gonar rake da take aiki a ciki babu tausasawa sasarin dake wuyanta na matuƙar shaƙe numfashita. Cikin hali da take a waya gari Anatsacia ta rasu sakamakon sarƙafewar da wuyanta ya yi.
Comments
Post a Comment