Min menu

Pages

Wasu manyan kalubalen da yan nigeria ke fama dasu.

 Wasu manyan kalubalen da yan nigeria ke fama dasu..



Koda yake kasar Nigeria kasa ce da ta tara manyan abubuwa na birgewa wanda hakan yasa tayiwa sauran kasashen dake africa fintinkau..

Kamar ta bangaren dukiya, tarin mutane, yawan masu kudi, da kuma masu jin yare da yawa...


A takaice dai kasar nigeria tanada abubuwan birgewa masu tarin yawa dake cikin kasar, to saidai duk da wadannan abubuwan akwai wasu tarin kalubale dake damun yan kasar kuma suke ci musu tuwo a kwarya wanda har yanzu aka kasa shawo kansa sannan yan nigeria da yawa suna kuka dasu.


Ga jerin wasu daga cikin abubuwan da suke cuwa yan nigeria tuwo a kwarya..


Matsalar tsaro:- Matsalar tsaro wata katuwar matsala ce da take damun yan nigeria tsawon lokaci wanda har yanzu aka gagara shawo kanta, ada an samu yan boko haram wanda suka firnaci yankuna da dama kamar yankin maiduguri jihar Borno da kuma sauran yankuna irinsu jihar yobe, adamawa da sauransu.


Anyi kokari sosai domin kawar da wadannan yan boko haram din, to saidai kafin a kawar dasu sai gashi wasu sun bayyana kamar yan fulanin daji, da kuma masu garkuwa da mutane wanda suke suke tare hanya ko kuma su shiga har gari su dauke mutane sannan dole sai an biya kudin fansa za'a sako mutum.

Wasu da dama sun dora laifukan ne akan gwamnati suna ganin kusan ita ce taki bada hadin kai wajen dakile faruwar irin wadannan ayyukan, mutane da yawa suna ganin cewa bai kamata kasar nigeria tana fama da matsalar tsaro ba kasancewar kasar a mataki na farko a jerin kasashen da suke da jami'an tsaro a africa..


Talauci:- Yan kasar Nigeria suna fama da tsananin talauci wanda mutane da yawa ke kwana da yunwa, hakan yasa wasu da dama suke bin barauniyar hanya ko kuma muce mummunar hanya wajen ganin sun samu abinda zasu ciyar da kansu..


Anyi ittifakin kusan kaso biyu na yan kasar a cikin uku suna fama da tsananin talauci kuma wai kasar tana daya daga cikin kasashe goman da suke da arziki a nahiyar ta africa..


Ilimi:- Yanzu kam harkar ilimi gaba daya ta rushe a nigeria domin makarantu dama sauran guraren da ake daukar karatu basa a gyare, sannan ga karancin malamai masu koyarwa ga yawaitar yajin aikin da ake yawan yi a kasar wanda ba karamin komar da kasar baya yayi ba a bangaren ilimi.


Abubuwan more rayuwa:- Yanzu kusan mutane da yawa baza su iya fada muku kwanakin da sukai rabon da suga wutar nepa ba ko kuma ace titunan da suke bi suna da kyau ba kuma wadannan suna daga cikin abubuwan more rayuwar da aka rasa su a nigeria..


Sauran sun hada da

Rashin aikin yi

Zaman banza

Da sauransu



Comments