Al'adar rawa akan garwashin wuta
Wannan wata al'adace da wasu al'umma na kasar Bulgaria suka shafe shekaru suna gudanarwa. Yayin wannan al'ada mai ban mamaki da suke kira da 'Nestinarstvo' wadda ke nufin 'rawa akan wuta' mutane kanyi tafiya akan garwashin wuta batare da sun koneba har sai wutar ta mutu.
Guraren bauta da kuma masu kokarin kare hakkin dan adam sunyi kokarin dakatar da wannan al'adar, wasu sun daina amma wasu suna yi domin har yanzu ana gabatar da ita a wasu yankuna na kasar.
Wannan al'ada ana farata ne yayin da rana ta fadi, a lokacin da jagoran zai fito da farar Riga da kuma jan kyalle a daure a kugunsa.
Domin kallon bidiyon duba kasa
Comments
Post a Comment