Min menu

Pages

Kabilar da basa auren mace sai an gwada ta anga ko bata rasa budurcinta a waje ba

 

 Kabilar da basa auren mace sai an gwadata anga ko bata rasa budurcin ta ba



Al'adu yawa gare su a duniya kamar yadda kasashe da yankuna da kuma yaruka suke da yawa.


Wannan yasa al'ada da dabi'un wasu yankunan ya bambanta dana wasu, yau cikin zagayen namu munyi karo da wani yanki wanda suke yiwa mace gwaji domin su tabbatar da cewa budurwa ce ko kuma ta rasa budurcin ta kafin sukai ga batun aure.


Kabilar umkhosi dake Africa ta kudu suna gabatar da wani shagalin biki na al'ada wanda suke yin abubuwa da yawa a cikin bikin ciki harda gwaji na tabbatar da mace a matsayin budurwa.


Duk karshen shekara ana gwada yan mata da yawa domin a gane wacce ta taba zina da kuma wacce bata taba zina ba, idan gwaji ya nuna kin taba zina shikenan kin zama abar nunawa tare da dariya a gari kuma da wuya a samu wanda zai aure ki idan kuma baki taba ba shikenan kin huta.



Comments