Jerin kasashen Africa da suka hana yin bleaching da sayar da mayukan bleaching din
Bleaching wani abu ne da mafiya yawan mata ke yi domin su mayar da kalar fatarsu zuwa baka, mafi akasari matan da suke bakake ne sunfi yinsa duk da cewar akwai wasu daga cikin fararen ma suna yi.
Anfi samun masu yin bleaching daga cikin mata domin ba'a cika samu daga gurin maza ba a da kenan, amma yanzu suma mazan sun baci sosai da yin wannan halayyar ta yin bleaching ko kuma muce shafe shafe.
Shi kansa bleaching din ya kasu kashi kashi ne, akwai wanda suke amfani da mai na shafawa akwai kuma masu amfani da sabulu na wanka wasu ma allura ake musu ta bleaching din.
Likitoci da yawa sunyi bayani akan cewa yin bleaching yanada matukar illa sosai ga fatar jiki domin yana kashe garkuwar fata da kuma sauran abubuwa wanda koda ciwo mutum yaji da wuya gurin ya gyaru, sannan yana matukar bata fata.
Yau cikin shirin namu zamu zayyano muku jerin kasashen da suka hana yin bleaching sannan suka mayar dashi a matsayin doka, saidai daga cikin kasar da zamu kawo za kuga harda Nigeria.
A zahirin gaskiya a Nigeria ma an hana yin bleaching a dokance amma dake ba wani tsaurarawa akai ba yan kasar suna yin kayansu wannan kuwa ya faru ne saboda yadda kamfanonin wadannan mayukan suke bada cin hanci da kuma sauransu.
Dan haka ga jerin kasashen da aka hana sayarda mayukan bleaching da kuma yin bleaching din a dokance.
1. Ghana 🇬🇭
2. Rwanda 🇷🇼
3. Tanzania 🇹🇿
4. Côte D'Ivoire 🇨🇮
5. South Sudan 🇸🇸
6. Kenya 🇰🇪
7. Nigeria 🇳🇬
Comments
Post a Comment