Musayar yan wasa a yau Laraba makomar: Benzema, Smith Rowe, Enrique, Caicedo, Gnonto, Pulisic, Asensio, Weghorst, Maddison, kone
Ga kanun labaran
Ga cikakken labarin
Dan wasan gaba na Real Madrid Karim Benezema kungiyar kwallon kafa ta Al-hilal na tunanin daukarsa bayan tayin kwantiragin shekaru biyu na Euro miliyan 400 (£346m) zuwa Saudi Arabiya ga Dan kasar Faransa, mai shekaru 35. (ESPN)
Arsenal ba ta da niyyar siyar da Emile Smith Rowe, mai shekaru 22, a bazara kuma tana fatan dan wasan gaban Ingilan da ya ji rauni zai dawo cikin koshin lafiya a gasar cin kofin Turai na 'yan kasa da shekaru 21, (Athletic - subscription required)
Kocin da Tottenham Hotspur take zawarci Luis Enrique yana tattaunawa da zakarun Serie A Napoli, duk da haka, tsohon kocin Spain da Barcelona yana son zuwa kungiyar ta Premier. (Guardian)
Tottenham da Newcastle na fafatawa kan dan wasan tsakiya na Leicester James Maddison, mai shekaru 26, da kuma dan wasan gefe Harvey Barnes, mai shekaru 25, inda duka 'yan wasan na Ingila suka kai kusan fan miliyan 40. (Sun)
Yarjejeniyar tsakanin kocin Brighton Roberto de Zerbi da Moises Caicedo na daf da karewa inda dan wasan tsakiyar Ecuador mai shekaru 21 zai bar kungiyar a wannan bazarar. A halin yanzu kungiyoyi uku ne ke zawarcin Dan wasan inda Chelsea take kan gaba. (Fabrizio Romano)
Manchester City da Arsenal suna zawarcin dan wasan gaban Leeds United da Italiya Wilfried Gnonto, mai shekaru 19. (Calciomercato - in Italian)
Manchester United ba za ta sayi dan wasan gaban Netherlands ba Wout Weghorst, mai shekaru 30, da dan wasan tsakiyar Austria Marcel Sabitzer, mai shekaru 29, kan kwantiragin dindindin daga Burnley da Bayern Munich. (Mail)
Dan wasan Real Valladolid dan kasar Sipaniya Ivan Fresneda, mai shekaru 18, ya samu tayi mai tsoka daga Arsenal. (BILD - in Germany)
Dan wasan bayan Faransa Benjamin Pavard, mai shekaru 27, na shirin barin Bayern Munich bayan Inter Milan ta nuna sha'awarta a watan Janairu. (Fabrizio Romano)
Aston Villa na zawarcin dan wasan Real Madrid Marco Asensio, wanda ake sa ran zai bar kungiyar a kakar wasa ta bana. Dan wasan na Spain, mai shekaru 27, yana kuma jan hankalin Paris St-Germain, Arsenal da AC Milan. (Sun)
Liverpool na zawarcin dan wasan tsakiya na Borussia Monchengladbach dan kasar Faransa Manu Kone, mai shekarmu 22, inda farashin dan wasan mai shekaru 22 ya kai kusan Yuro miliyan 40 (£34.6m). (BILD - in German)
Juventus ce ke kan gaba wajen neman sayen dan wasan gaban Chelsea Christian Pulisic, mai shekaru 24, a kan dala miliyan 25 (£20.1m). (Mail)
Mai tsaron gidan FC Porto dan kasar Portugal Diogo Costa, mai shekaru 23, yana neman komawa Manchester United, yayin da dan kasar Sipaniya David de Gea, mai shekaru 32, shi ma yana sha'awar kulla sabuwar yarjejeniya da kungiyar. (Mirror)
Wolves ta bi sahun Chelsea da Crystal Palace wajen neman dan wasan gaban Gambia Adama Bojang, mai shekaru 19, wanda ke taka leda a kungiyar Steve Biko FC ta Gambia. (Standard)
Comments
Post a Comment