Musayar yan wasa a yau ranar Alhamis makomar: Mount, Barnes, Kane, Osimhen, Harrison, Palhinha, Kim, Nelson, Smith Rowe, Maddison, kounde
Ga kanun labaran
An shaidawa United kudin Osimhen bayan amincewa da daukar abokin wasansa Min-Jae, Arteta zai sallami Smith Rowe domin dauko Maddison, Arsenal naci gaba da shirinta na sallamar Yan wasan kimanin Takwas, United ce kan gaba wajen neman Mount, West Ham zata ci gaba da zama da Moyes, Barcelona ta shiga damuwa bayan kounde ya bayyana bukatar sa ta barin kungiyar, Madrid zata shiga zawarcin Robertson
Ga cikakken labarin
Manchester United za ta biya fam miliyan 55 don siyan dan wasan tsakiya na Chelsea da Ingila Mason Mount kuma tana da burin doke Liverpool da Arsenal kan daukar dan wasan mai shekaru 24. (Mail)
Mount zai tattauna makomarsa ta Chelsea a wata ganawa da za ai dashi da shugabannin kungiyar a mako mai zuwa. (90min)
Mount zai karkata hankalinsa izuwa Manchester United idan Chelsea ta yanke shawarar siyar da shi. (The Athletic - subscription required)
Aston Villa ce ke kan gaba wajen neman dauko dan wasan Leicester City Harvey Barnes, mai shekaru 25, dan kasar Ingila. (Guardian)
West Ham a wani bangaran kuma tana sha'awar dauko Barnes, da kuma dan wasan Leeds United ds Ingila Jack Harrison, mai shekaru 26. (Sun)
West Ham za su ci gaba da rike David Moyes a matsayin kocinsu kuma suna da niyyar mara masa baya ta hanyar zawarcin dan wasan Fulham da Portugal Joao Palhinha, mai shekaru 27, a matsayin wanda zai maye gurbin dan wasan tsakiyar na Ingila Declan Rice, mai shekaru 24. (Guardian)
Arsenal na shirin siyar da 'yan wasa kusan 14 a rukunin farko don samar da kudin sayan sabbin 'yan wasa takwas a manyan sake gina kungiyar a bazara - inda Dan wasan kasar Ivory Coast Nicolas Pepe, mai shekaru 27, yake daya daga cikin wadanda za su bar kungiyar. (Football.London)
Mikel Arteta a shirye yake ya bar dan wasan tsakiya na Ingila Emile Smith Rowe, mai shekaru 22, ya bar Emirates domin ya bada damar dauko dan wasan Leicester da Ingila James Maddison, mai shekaru 26. (Mirror)
Har ila yau Gunners din na sha'awar kara dan wasan gaban Torino da Paraguay Antonio Sanabria, mai shekaru 26, a kan fam miliyan 21.6. (La Repubblica via Mail)
An shaida wa Manchester United cewa dole ne ta biya fam miliyan 140 idan har tana son sayen dan wasan gaba na Napoli da Najeriya Victor Osimhen, mai shekaru 24, a bazarar nan bayan da suka amince da sayan abokin wasansa kuma dan wasan baya na Koriya ta Kudu Kim Min-jae, mai shekaru 26. (Il Mattino) ta Mirror)
Napoli na matukar kokarin shawo kan Kim ya rattaba hannu kan sabon kwantiragi kafin batun sakin ya fara aiki a wannan bazarar. (90min)
Duk da haka, dan wasan Tottenham da Ingila Harry Kane, mai shekaru 29, har yanzu ya ci gaba da zama zabin farko na dan wasan gaba da Manchester United zati kokarin zawarci a bazara. (Guardian)
Aston Villa na son tabbatar da rantaba dogon kwantiragin dan wasan gaban Ingila Ollie Watkins, mai shekaru 27, da dan wasan tsakiya na Scotland John McGinn, mai shekaru 28, da sabbin kwangiloli kafin bude kasuwar musayar 'yan wasa. (Telegraph - subscription required)
Feyenoord ta na daf da rasa kocinta Arne Slot Wanda kungiyar Tottenham ke ci gaba da bibiya. (Football Insider)
Real Betis na iya komawa neman dan wasan tsakiyar Leeds United dan kasar Sipaniya Marc Roca, mai shekaru 26, idan kulob din na Yorkshire ya bar gasar Premier izuwa relegation. (Estadio Deportivo)
Arsenal ta yi wa dan wasan tsakiyar Ingila Reiss Nelson sabon kwantiragi har zuwa shekarar 2027, tare da zabin karin shekara, amma kuma dan wasan mai shekaru 23 yana samun tayi daga wasu kungiyoyin Premier, Italiya da Spain. (Fabrizio Romano)
Kocin Swansea Russell Martin da baki ya amince ya zama sabon kocin Southampton. (Sky Sports)
Martin, mai shekaru 37, ya amince da kwantiragin shekaru uku don zama sabon kocin Southampton, inda kulob din da ya koma gasar Premier zai sanar da nadin nasa nan da kwanaki masu zuwa. (Sun)
Barcelona ta kadu da rade-radin cewa dan wasan baya na kasar Faransa Jules Kounde, mai shekara 24, na son barin kungiyar, shekara guda da komawarsa daga Sevilla. (90min)
Qatar Sports Investments, wacce ta mallaki Paris St-Germain, ta yi yunkurin siyan Santos mai rike da kofin Seria A Brazil sau takwas. (Mirror)
Real Madrid ta shiga zawarcin Dan wasan baya na Liverpool da Scotland Andrey Robertson a yunkurinta na neman Wanda zai maye gurbin Mendy. (Athletic - subscription required)
Comments
Post a Comment