Musayar yan wasa a yau ranar Lahadi makomar: Mbappe, Kane, Kudus, Osimhen, Lukaku, Zaha, Suarez, Gvardiol, Laporte, Lavia, Hojlund
Ga kanun labaran
Chelsea da kulob din Al-Hilal na Saudiyya sun fara yunkurin dauko dan wasan gaban Faransa Kylian Mbappe, mai shekaru 24, wanda bai yi tafiya da Paris St-Germain ba a rangadin da suke yi a Asiya. (RMC Sport - in French)
Al-Hilal dai sun yi wa Mbappe irin tayin da suka yi wa Lionel Messi na Yuro miliyan 400 a shekara (£346.3m) har zuwa shekarar 2026, duk da cewa yana da yarjejeniyar komawa Real Madrid a matsayin kyauta a bazara mai zuwa. (Nicolo Schira)
Mbappe ya shirya tsaf domin barin PSG a kakar wasa mai zuwa bayan da zakarun Faransa suka siyar da shi ranar Juma'a. (Sky Sports)
An hango matar Harry Kane a Munich, tana neman kadarori da makarantu gabanin yuwuwar komawa Bayern Munich daga Tottenham zuwa Bayern Munich dan wasan Ingila mai shekaru 29. (Bild - in German; subscription required)
Chelsea ta tuntubi Ajax don nuna sha'awarta ta siyan dan wasan Ghana Mohammed Kudus, mai shekaru 22.
Tattaunawar kwantiragin Victor Osimhen da Napoli na ci gaba da kasancewa cikin tsaka mai wuya, wanda hakan ya bude kofa ga Chelsea ko Manchester United wajen siyan dan wasan Najeriya mai shekaru 24. (Corriere dello Sport, via Goal)
Inter Milan ta yi imanin cewa yanzu ba zai yiwu a yi tunanin dawo da Romelu Lukaku kulob din daga Chelsea ba bayan dan wasan Belgium din, mai shekaru 30, ya tuntubi abokan hammayarsu AC Milan da Juventus kan yiwuwar komawa kulob din. (Gazzetta dello Sport - in Italian)
Galatasaray ta taya dan wasan gaban Ivory Coast Wilfried Zaha, mai shekaru 30, wanda ke zaman kyauta bayan kwantiraginsa na Crystal Palace ya kare, kwantiragin kusan fam miliyan 8 a shekara. (Mail on Sunday)
Dan wasan gaban Uruguay Luis Suarez, mai shekaru 36, a shirye yake ya biya daga aljihunsa domin ya bar Gremio ya sake haduwa da tsohon abokin wasan sa na Barcelona Lionel Messi a Inter Miami. (ESPN, via Sport - in Spanish)
An gaya wa Manchester City cewa za ta biya RB Leipzig cikakken farashin fan miliyan 87 don sayen dan wasan bayan Croatia Josko Gvardiol, mai shekaru 21. (Sunday Mirror).
Crystal Palace na tunanin zawarcin dan wasan bayan Manchester City dan kasar Sipaniya Aymeric Laporte, mai shekaru 29. (Star Sunday).
Manchester United na shirin daukar karin shekara kan tsawaota kwantiragin dan wasan baya na kasar Ingila Aaron Wan-Bissaka, mai shekaru 25, duk da cewa Palace na sha'awar sake siyan shi. (Sunday Sun)
Fulham na shirin kashe sama da fam miliyan 30 wajen siyan sabbin 'yan wasan baya biyu - dan kasar Ghana na Southampton Mohammed Salisu, mai shekaru 24, da dan wasan bayan Ajax dan Najeriya haifaffen Italiya Calvin Bassey, mai shekaru 23. (Sunday Telegraph)
Dan wasan Jamaica Michail Antonio, mai shekaru 33, yana sha'awar barin West Ham don ya koma Al-Ettifaq ta Steven Gerrard a bazara. (Football Insider)
Dan wasan gaba na Ingila Ivan Toney, mai shekaru 27, yana tunanin canza wakilinsa, alamar da ke nuna cewa yana neman barin Brentford tun kafin dakatarwar da aka yi masa na tsawon watanni takwas saboda karya dokar caca a watan Janairu. (Sunday Sun)
Manchester United ta yi imanin cewa farashin £50-60m zai kasance daidai darajar dan wasan Atalanta na Denmark Rasmus Hojlund, mai shekaru 20. (Insider Football).
Kocin Brighton Roberto De Zerbi ya yi tsokaci kan yuwuwar yarjejeniyar musaya da Levi Colwill, inda Chelsea ta yi amfani da dan wasan bayanta na Ingila, mai shekaru 20, don taimaka mata wajen sayen dan wasan tsakiyar Seagulls na Ecuador Moises Caicedo, mai shekaru 21. (Talksport).
Har yanzu Liverpool na tuntubar Southampton kan cinikin dan wasan tsakiyar Belgium Romeo Lavia, mai shekaru 19, kuma suna fatan za a iya cimma yarjejeniya a karshen watan Yuli. (Football Insidr)
Southampton ta ki amincewa da sabon tsarin da Newcastle ta yi na sayen dan wasan Ingila na 'yan kasa da shekaru 21 Tino Livramento, mai shekaru 20. (Talksport).
Dan wasan Watford dan kasar Senegal Ismaila Sarr, mai shekaru 25, yana dab da komawa Marseille duk da sha'awar da Everton ke yiwa Dan wasan, wanda hakan ba zai shafi zawarcin dan wasan Sarr ba, da dan wasan Sheffield United Iliman Ndiaye, mai shekaru 23. (FootMercato - in French)
Manchester United za ta sanar da sayen 'yan'uwa tagwaye Jack da Tyler Fletcher, 'ya'yan tsohon dan wasan tsakiya na United Darren Fletcher, daga Manchester City, a yarjejeniyar da ta kulla da 'yan shekaru 16 dan a Burtaniya. (Fabrizio Romano)
Comments
Post a Comment