Musayar yan wasa a yau ranar Alhamis makomar: Mbappe, Lavia, Hojlund, Cancelo, Kane, Van de Ven, Caicedo, Hojbjerg, Fred, Lenglet, Gvardiol
Ga kanun labaran
Ga cikakken labarin
Dan wasan gaba na Paris St-Germain da Faransa Kylian Mbappe, mai shekaru 24, ya shaida wa Chelsea cewa zai yi shirin shiga kwantiragin shekara guda idan har zai iya komawa Real Madrid kyauta a bazara mai zuwa. (Sport in Spanish)
Manchester United na son dan wasan Southampton dan kasar Belgium Romeo Lavia, mai shekaru 19, bayan da Liverpool ta yi watsi da zawarcin Dan wasan. (Independence)
Za a iya jinkirta siyan dan wasan Atalanta dan kasar Denmark Rasmus Hojlund mai shekaru 20 da Manchester United ta yi har zuwa karshen wannan makon bayan ya isa Manchester daga baya kamar yadda aka tsara ranar Talata. (Manchester Evening News)
Dan wasan gaban Ingila Harry Kane, mai shekaru 30, zai iya barin wani kaso mai yawa na albashinsa na Tottenham domin ya taimaka ya koma Bayern Munich. (Bild - German)
Tottenham ta amince da yarjejeniyar sirri da dan wasan baya na Wolfsburg dan kasar Holland Micky van de Ven, mai shekaru 22. (Talksport)
Tottenham na neman kammala siyar da dan wasan tsakiya na kasar Denmark Pierre-Emile Hojbjerg mai shekaru 27 ga Atletico Madrid, wanda kimarsa takai fan miliyan 30. (90min)
Inter Milan na zawarcin dan wasan bayan Arsenal dan kasar Japan Takehiro Tomiyasu, mai shekaru 24. (Gazzetta dello Sport - a Italian)
Barcelona na tattaunawa da Manchester City kan neman dan wasan bayan Portugal Joao Cancelo mai shekaru 29. (Talksport)
Manchester United ta fara tattaunawa da Real Sociedad game da siyar da dan wasan tsakiyar Netherlands Donny van de Beek, mai shekaru 26, wanda zai taimaka wajen sayen dan wasan Fiorentina dan kasar Morocco Sofyan Amrabat mai shekaru 26. (Mail)
Chelsea na fuskantar fafatawa kan dan wasan tsakiyar Brighton dan kasar Ecuador Moises Caicedo, mai shekaru 21. Wani kulob da ba a tantance ba ya yi tayin sama da na Chelsea fan miliyan 80. (Athletic - subscription required)
Chelsea za ta kai ingantaccan tayi kan Caicedo, wanda Brighton ta kimanta kusan fan miliyan 100. (Sky Sports)
Aston Villa na son dan wasan tsakiyar Amurka Tyler Adams, mai shekaru 24, kuma a shirye take ta biya fam miliyan 25. (Mail)
West Ham na neman madadin dan wasan tsakiya na Southampton James Ward-Prowse, mai shekaru 28, bayan da da kungiyar taki amincewa da tayin fam miliyan 30. (Sky Sports)
Al-Nassr zata biya Yuro miliyan 15 (£13m) kan dan wasan bayan Barcelona dan kasar Faransa Clement Lenglet, mai shekaru 28, wanda kuma Tottenham ke nema.(Sport - in Spanish)
Luton ta amince ta biya fam miliyan 2.5 tare da kari don siyan golan Blackburn mai shekaru 30, Thomas Kaminski. (Athletic - subscription required)
Inter Milan za ta daukaka tayin dan wasan West Ham dan kasar Italiya Gianluca Scamacca mai shekaru 24 zuwa £21.5m. (Evening Standard)
Dan wasan Brazil Willian, mai shekaru 34, ya samu tayi daga kungiyar Al-Shabab ta Saudiyya makonni biyu bayan ya amince da kwantiragin shekara daya da Fulham. (Athletic - subscription required)
Bournemouth tana cikin tattaunawa mai zurfi kuma tana shirin kai wa Wolves cinikin £25m kan dan wasan tsakiyar Bristol City dan Ingila Alex Scott. (Telegraph - subscription required)
Everton na neman dan wasan gaban Southampton dan Ghana Kamaldeen Sulemana, mai shekaru 21, a matsayin madadin dan wasan gefe na Leeds United dan kasar Italiya Wilfried Gnonto mai shekaru 19. (Insider football)
Besiktas na dab da sayen dan wasan gaban Arsenal dan kasar Ivory Coast Nicolas Pepe, mai shekaru 28. (Transfermarkt - in English)
Besiktas na tattaunawa da dan wasan tsakiya na Ingila Alex Oxlade-Chamberlain, mai shekaru 29, bayan kwantiraginsa na Liverpool ya kare a bazara. (Express)
Nottingham Forest da West Ham na zawarcin dan wasan gaban Paris-St Germain dan kasar Faransa Hugo Ekitike mai shekaru 21. (RMC Sport in France)
Galatasaray har yanzu tana sha'awar sayen dan wasan tsakiya na Manchester United dan kasar Brazil, mai shekaru 30, Fred a wannan bazarar. (Mail)
Comments
Post a Comment