Min menu

Pages

Yanda zakai maganin matsalar shan caji a wayarka

YANDA ZAKAI MAGANIN MATSALAR SHAN CAJI

Assalamu alaikum warahmatullahi wabarakatuhu ƴan uwa barkanmu da wannan lokaci sannan kuma barkanmu da sake saduwa a cikin wannan sabon darasin da muke kawo manyan Apps.



WANNE MANHAJA CE WANNAN?

Haƙiƙa wannan manhaja zata burge duk me amfani da wayar hannu musamman manyan wayoyin Android wanda ze wahala kaga bakada matsalar yawan ƙarewar batir batare da wani sababi ba a don haka a wannan darasin da mukai munzo muku da wani App wanda ze rabaka da wannan matsalar da yardar Allah.

DALILIN KAWO WANNAN APP ƊIN

Duba da yanda ƙorafin al'umma yake sake yawaita kan cewa" menene dalilin ƙarewar cajin wayarmu?" ko kuma meyasa wayata batabriƙe caji" ? A don haka mukai ƙoƙari muka lalubo abunda ke maganin wannan matsalar da kuma hana abunda ke saka wannan matsalar ta hanyar amfani da wannan Application da halastacce ne a Google PLAYSTORE. Sannan wani abun burgewa da wannan App ɗin yanada wasu abubuwa da yawa, kamar idan ka saka caja mara kyau a wayarka ze sanar dakai cewa wannan cajar ba me kyau bace ya kamata ka canza ka saka me asalin kyau domin kiyaye ingancin batirinka.

Kamar yanda mukai bayani a bidiyon mun san cewa ƴan uwa zasu fahimta kuma ze burgesu.

idan kanasan Sauke wannan App ɗi  zaka iya

Danna nan

Danna nan

Bayan ya kaika Google PLAYSTORE kawai zaka danna Install sannan seka fara aiki dashi kanar yanda mukai bayaninsa a aikace da kuma ta hanyar sharhi.

Wasalam alaikum,

mun gode 

Comments