Min menu

Pages

Muhimman App guda 2 a wannan watan

MUHIMMAN APP GUDA BIYU A WANNAN WATA


Assalamu alaikum warahamatullah, ƴan uwa barkan mu da wannan lokaci, sannan kuma da sake saduwa a wannan sabon darasin.Wanda a shine muke kawo muku muhimman abubuwan da suka shafi Fasahar zamani, musamman abinda ya shafi wayar hannu.

A don haka batare da ɓata lokaci ba zamu shiga cikin bayanin App na Farko wanda nasan ze burge duk wanda yake bibiyar harkokin da ya shafi Fasahar zamani.

DALILIN KAWO WANNAN APP ƊIN?

Babban dalilin kawo wannan App ɗin shine, duba da yanda mutane suke shan wahala yayin da wayarsu ta cika da Applications harma wataran kaga tana yin nauyi a yayin da kake amfani da ita.

To a don haka muka nemi mafita kan yanda mutane zasu magance wannan Babbar matsalar ta hanyar yin amfani da wannan Application ɗin wanda muka gabatar da bayanin sa a bidiyo.

BABBAN AIKIN APP (CANTA)


Kai tsaye babban aikin wannan App ɗin shine a duk lokacin da wayarka ta cika da Apps kuma Kana gudun ka su ɗaukar maka waje, wato Space, kawai zaka saka wannan App ɗin ne sannan zaka goge dukkan App ɗin da kake so batare da ya tafi duka ba, ze tafi cikin wannan App ɗin me suna Canta ya aje kansa, kai kuma a duk lokacin da kake bukatarsa kawai zaka sake dawo dashi, ta dai cikin App ɗin, wanda ze taimaka maka batare da ka sake zuwa Google PLAYSTORE ba kayi installing ɗin sa ba.

Kaga wannan zai taimaka maka wajan tattalin Mb ɗinka, sannan kuma ze taimaka maka wajen tattalin Space na wayar ka da kuma dawo dashi cikin sauki.

Idan kaje downloading zakaga ya kaika nan, a don haka hoton da na saka, zaka danna inda na zagaye.




Kada na tsawaita a zance na

Idan kana san downloading wannan App ɗin..






BAYANIN APP NA BIYU ( DUAL WALLPAPER)


Kamar yanda muka sani a duk lokuta zaka so ka dinga canza yanayin wayarka ta hanyar saka mata wasu App ko kuma wallpapers da dai sauransu.

Kamar yanda muke yawan fada a baya, cewa dukkan dan Adam yana son ya dinga ganin canji a rayuwarsa, musamman a lokacin da yake amfani da wani abu guda Kuma ya dauki tsawon lokaci yana aiki da wannan abun, tofa tabbas zeji gajiya wa ze kuma bukaci canji.

A don haka ne muka zo maku da wannan App ko kuma nace wannan Wallpaper wadda zata canza maka wayarka ta gyara maka screen ɗin wayarka cikin kankanin lokaci ta zama abun burgewa da kuma abun kayatarwa.

Wani abun burgewa da wannnan App din ze baka dama ka saita Fuskar da kake so wayarka ta koma da dare da kuma wadda kake so ta koma da Rana.
Wanda wannan ze taimaka maka wajen kare idanun ka daga haske na waya da kuma kara musu lafiya.

Idan Kanasan downloading wannan App danna..


A wannan lokacin ne zamu kawo karshen darasin, idan wannan darasin ya burge ka kada ka manta ka danna masa Like daga bisani kai mana Share domin ƴan uwa su gani suma su amfani

Wasalam,
Sai anjima


Comments

2 comments
Post a Comment

Post a Comment